Barka da Zuwa Makarantan Lorewa

Lorewa dandali ne na koyo a yanar gizo ga matan Arewa, da zai isar da fasaha mai mahimmanci da ilimi zuwaga matan arewa, yan mata da matasa a duk fadin duniya. Wannan dandali ne na matan arewa domin su samu kwadayin koyo da  koyarwa.

Drag to resize

Barka da Zuwa Makarantan Lorewa

Lorewa dandali ne na koyo a yanar gizo ga matan Arewa, da zai isar da fasaha mai mahimmanci da ilimi zuwaga matan arewa, yan mata da matasa a duk fadin duniya. Wannan dandali ne na matan arewa domin su samu kwadayin koyo da  koyarwa.

Drag to resize

Barka da Zuwa Makarantan Lorewa

Lorewa dandali ne na koyo a yanar gizo ga matan Arewa, da zai isar da fasaha mai mahimmanci da ilimi zuwaga matan arewa, yan mata da matasa a duk fadin duniya. Wannan dandali ne na matan arewa domin su samu kwadayin koyo da  koyarwa.

Labarinmu (Our Story)

The Bravery of the Northern Woman

A matsayin kamfani na horarwa, Media da dijital wanda ya dauki nauyin mata da yawa daga Arewa sama da shekaru 10 aiki, mun ga irin karfi, hikima da basirar Matar Arewa kuma muna godiya da hakan.

Don haka muka yanke shawarar gina dandali ga Matar Arewa da fadada ilimi da horon da muke ba wa ‘yan kadan don isa ga dubbai da miliyoyi. Sannan kuma mun tambayi kanmu, ta yaya iyayenmu mata, kakanninmu, matan sana’o’in hannu, ’yan kasuwa mata, masu horar da mata, shugabannin al’umma, za su iya mika basirarsu da iliminsu, ba ‘ya’yansu mata kawai ba, amma ga sauran ‘yara da mata a fadin Arewa?

An haifi LOREWA. Amma ta yaya sunan ya samo asali?

LORE + AREWA = LOREWA.
LORE bisa ga ƙamus na Oxford yana nufin - ƙungiyar al'adu da ilimi akan wani batu ko wani rukuni na musamman, yawanci wucewa daga mutum zuwa mutum ta hanyar baki. Kuma tabbas AREWA tana nufin Arewa.

To ka ga da gangan aka yi mana Lorewa. A duk lokacin da kuka ga LOREWA, ku tuna, wannan shine dandalinmu kuma yana nufin  Koyon Dijital ga Matar Arewa, don koyarwa da koyo.

Haka nan kuma mu ambaci cewa wannan dandalin Lorewa, tambari mai kyau, darussan mu, aikin gaba daya matan Arewa ne suka gina shi, ba shakka mun samu wasu ’yan tsirarun mazaje a cikin wannan tawaga da wasu makusanta da abokan arziki daga sassan Najeriya, amma. mu matan Arewa mun fi kashi 90%. Wannan aiki ne mai hawa da sauka, amma muna ci gaba da nunawa duniya cewa baiwar ‘yar Arewa ba ta da iyaka.

Tare da wannan dandali, muna sa ran haɗa ɗalibai, iyaye mata, 'ya'ya mata, makwabta, abokai da al'ummomi. Idan za ku iya koyar da wani abu, wani yana buƙatar wannan ilimin don ingantacciyar rayuwa da ingantaccen aiki.

Labarinmu (Our Story)

Jarumtar Matan Arewa

A matsayinmu na kamfani wanda ya ƙunshi ‘yan mata da yawa na Arewa, mun gabatar da hanyoyin horarwa na shekaru 10 kuma mun yi matuƙar godiyan ƙarfi da girman da ke ƙarƙashin ƙasa. Muna ganin kanmu kowace rana muna ƙara gaba don ƙaunan kula da wasu. Tunaninmu a kullum, ta ya zamu ƙarawa Matan Arewa ƙarfi? Ta yaya za mu faɗaɗa ilimi da horon da muke ba mutane ƙalilan don isa ga dubban mutane? Ta yaya za mu tallafa a wajen  ba da gudummawa ga waɗannan al'ummomin da muke aiki domin su ba dare ba rana?

Waɗannan tambayoyin sun haifar da kafuwar LOREWA - wacce take wakiltar LORE (KOYI) + AREWA, ma’ana koyo ga Matan Arewa. Tare da wannan dandalin, muna fatan haɗa mahaɗan masu koyo, uwaye, 'ya'ya mata, maƙwabta, abokai da al'ummomi. Idan za ku iya koyar da wani abu, wani daga can yana buƙatar wannan ilimin don ingantacciyar rayuwa da ingantacciyar aiki

Write your awesome label here.

Matan Arewa Miliyan Arba'in

A ƙididdige, matan Arewa sun haura miliyan Arba’in a faɗin jihohi 19 na Arewacin Najeriya. Babban damarsu shine Koyo da kuma ƙarfafa su don ɗaga darajar Arewa gaba ɗaya.

Lorewa- Dandalin yanar gizo na Koyo ga Macen Arewa

Lorewa shine dandalin yanar gizo na koyo ga macen Arewa, inda dukkan darussan matan arewa ne suka koyar, a harshen Hausa. Abu mafi kyawu sake koyo da yarenmu na gida, samun damar haɗuwa da namu.

Darussa daga kewayen bunƙasa kai, kasuwanci, rayuwar iyali, lafiyar jiki, harkan noma, yara da dai sauran su.

Macen Arewa a yanzu na da dandalin raba ilimi zuwa ga yawan matan arewa a faɗin Duniya. Ku yi rajista a yau ku fara koyo.

Lorewa cikakkiyar kamfani ce mai rajista a Najeriya.
Write your awesome label here.

Ana Kiran mu ‘Yan Kasuwa na Jama’a

Mutane da yawa na kiranmu masu aiki ga al’umma

Eh wannan haka yake. Muna canza yadda matan Arewa ke koyo, karatu tare da samar da arziki ga malamai, ma’aikata, al’umma, da masu hannun jari. Muna yin wannan Ɗalibi ɗaya a lokaci guda. A shekaru masu zuwa, Al’umman Arewa za su zama fuskar dijital na Afirka.
Write your awesome label here.

Hadafinmu

Yawan Taron al’umman Arewa da za a isa ga nan da shekara biyar
254+
Yawan malaman da za su koyar nan da shekara Biyar
2000
Matan Arewa da za a koyar nan da shekara Biyar
2M

Yawan ma’aikatan da za a ɗauka a faɗin yankunan Arewa


200+

Shiga Sahu -  Yi bambanci

Ba abunda ya fi kyau kamar haɗin da ya zo wurin bada ilimi ta hanyar amfani da ƙarfin fasahar dijital, yare da abubuwan watsa labarai. Iyayenmu mata na Arewa, dattawa, malamai, ‘yan kasuwa, malaman makaranta suna da dandalin isar da iliminsu ga Duniya. Lorewa shine hanyar zuwa duniyar dijital.

Akwai sarari ga kowa. Danna ɗaya daga madannin da ke ƙasa don kasancewa tare da mu…
Zama Mai Koyarwa
Ki zama abokiyar tarayya
Ki zama mai tallafawa
Ki zama mai koyo

Koyarwa da Samu

Ki Raba Ilimiinki a yau ki fara samu. Wani a can yana buƙatar Ilimi ko ƙwarewar da kike da shi don inganta damar su ta cin nasara. Ki zama Jarumarsu.
Za a iya amfani da dandalin Lorewa ku horar da mata a unguwarku. Ko Kungiyar tallafawa al’umma mai zaman kanta ne, Kamfani, mai fada a ji, makaranta ko wani mutum, za mu iya tsara muku shafi na musamman domin hada ku da masu bibiyar ku.

Rubuta Sunanku da Zinare, Har Abada.

Horar da 'ya mace guda ku canja dukkan zamani. Ka zama mai tallafawa a Lorewa domin ingata rayuwar wasu. Ku tambaye mu yaya? Ku kira +2348067153900 ko ku yi mana email a [email protected]

Ku Dauki Darasi

Ba wanda zai iya dauke illiminki daga wurinki, wanda shine daya daga cikin bangarorin koyo da yafi daukar hankali. Ki samu takaddar kammalawa da sa hannun abokan tarayyar mu.
AL’UMMAR AREWA DA ZA A ISAR WA SAƘON
254+
MALAMAN DA ZA SU KOYAR
2000+
MATAN DA ZA A KOYARWA A NAN DA SHEKARA 5
2,000,000
MUTANE MASU FASAHA DA ZASU HADU SUYI AIKI TARE
200+

Board of Advisors & Executive Team

Working Together for The Greater Good.

Eberechi Okereke

Founder

Maryam Bukar Hassan

Co-Founder

Hukumar Masu Bada Shawara a Lorewa
(Board of Advisors)

Maimuna Mohammed Danfulani
Eberechi Okereke
Maryam Bukar Hassan
Hon. Stella Okotete
Dr Amina Aminu Dorayi
Maryam Lemu
Hon. Munira Suleiman
Maryam Laushi
Maryam Lawal
Hajiya Madina Dauda
Hon. Munira Suleiman
Dr Amina Aminu Dorayi

Abokan Tarayya
(Strategic Partners)

Hon. Munira Suleiman
Non-Executive Director 
Aisha Bashir Tukur
Member, Board of Advisors
Hon. Amina Ilyasu
Executive Director
Dr Amina Aminu Dorayi
Member, Board of Advisors
Drag to resize

Meet Our Team

Working behind the scenes for the greater good

Maryam Abdulrahman
Content Development Officer
Fatima Baba
Business Development Officer
Nuriya A. Jumare
Instructor Manager
Nafisa Abdul
Team Lead / Creative Director 
Aisha Bashir
Content Development Officer / Quality Assurance
Aisha Tajudeen Muhammad
Media Production Team
Zara Ingawa
Content Development Officer
Sahar Abdul-hamid
Content Development Officer
Habiba Manzo
Senior Project Manager
Fatima Suleiman
Content Development Officer
Abdullahi Kwale
Content Development Officer

A cikin Labari

Danna ko wani madannin da ke ƙasa don ƙarin bayani
Danna kuyi Chatting damu
Danna ku kira mu
Drag to resize

Hear from our colleagues

I am one of the founding staff of Lorewa Academy, having been trained extensively over the last 1-year. I work with many instructors and I am so proud of what we do everyday at Lorewa. We believe the Northern woman can be digital and we assist many to accomplish that dream. I look forward to onboarding you someday at Lorewa.   
HIDAYA AMINU
As a founding partner and instructor at Lorewa Academy, I have out up my first course and working on the next. We are building the largest digital learning platform for the Arewa Woman, anywhere in the world. The courses are well produced, educating and engaging. The team at Lorewa are doing something great.  
ALHANISLAM
I am simply amazed at the culture at Lorewa and the professionalism with which the Lorewa team handles their instructors and learners. They have everything you need to go digital as a woman. I created my course in a matter of days, and today I can reach more people and share the little knowledge I have.  
Khadija Muhammad