Adon Cikin Gida (Fundamentals of Interior Decor)

  • Malama: Khadija Muhammad
  • Mataki: Na Tsakiya
  • Sashe: 11
Write your awesome label here.
Game da darasi
Adon gida da fili abu ne da ke ƙara kyan wuri amma ba kowa ya san yanda ake yi ba. Tabbas ƙyale-ƙyalen gida ya fito ras yana ɗaya daga cikin abunda mace yakamata ta koya. Wannan darasin ya zo muku da abubuwa da dama na adon cikin gida, fara daga yanda ake gyara filin gida har yanda za a yi amfani da haske wajen ƙawata cikin gida.
  • Lokacin Bidiyo: 48:58mins 
  • Takardar Kammalawa: Akwai

Abubuwan da ke Ciki

  •  Bidiyon Kallo guda 11
  • Jarrabawa
  • Takardar Kammalawa

Game Da Wannan Darasin  

Wanna darasin na ƙunshe da abubuwan da ya kamata ku sani game da adon cikin gida da yanda za a sarrafa wasu abubuwan adon cikin gida ba tare da an sayo su a kasuwa ba, abubuwa kamar su pilon jerawa a  palo da bargon yara da dai sauran su

Fahimta

A wannan darasin za a koyi yanda ake ƙawata kayan adon cikin gida domin kwalliya. za a koyi yanda ake haɗa pilo, bargon yara, ire-iren kayan kwalliyan bango, da yanda ake amfani da haske da sauransu.

Darussan da ke Ciki

ga malamarku

Khadija Yaya

Khadija yar makarantar jami'a ce wanda take samun nishadi wajen yin kayan adon gida da kuma pilulluka. Ta kwashe shekaru masu yawa tana yin sana'ar adon cikin gida. Tayi wannan darasin ne domin koyar da mutane sana'ar adon gida da fili domin ilimantar da al'umma.
Patrick Jones - Course author