Ba Nakasasshe Sai Kasasshe (Coping Mechanism)

  • Malama: Fatima Ahmed
  • Mataki: Mai sauƙi
  • Sashe: 9
Write your awesome label here.
game da darasi
A bangarenmu na Arewa, ba kowa ne ya san abu game da 'Ya'ya masu bukata ta musamman ba. Wasu lokutan ana gurgunta fahimta don ba a san me ke kawo samun irin wannan yara ba, wasu kuwa suna ganin babu hanyar kare kai bare a san sanadi. Wannan darasi zai yi bayani dalla-dalla game da cututtukan, irin bukatar da suke nema da hanyoyin kare kai daga samun irin wannan yara.
  • Lokacin Bidiyo: 45:57mins 
  • Takardar Kammalawa: Akwai

Abubuwan Da Ke Ciki 

  • Bidiyoyin Kallo Guda 11 
  • Jarrabawa
  • Takardar Kammalawa 

Game da Wannan Darasin

A wannan darasin za ku fahimci abunda ake nufi idan an ambaci Yara masu bukata ta musamman, za ku san kalubalen da ke bibiyan kula da wadannan yara da yanda za a kare kai.

Fahimta

A cikin darasin nan za ku fahimci yara masu bukata ta musamman na da baiwan da bai kyautu ace an mayar da su nauyin da mutum ba zai iya dauka ba, hakazalika za ku fahimci tarin hidiman da ke tattare da kula da yara masu bukata ta musamman.

Darussan da ke Ciki 

GA MALAMARKU

Fatima Ahmed

Sunana Fatima Ahmed. Uwa kuma Mai Kullawa da yara Biyu masu bukata ta musamman.Ina da aure kuma ina yin sana’oina. A hakane na bude Haven homes Foundation, ddlgifts, kuma ni certified mixologist ce. Na samu Degree a Arts in History,na kuma samu certificate a computer studies,Cisco software & hardware certificate, higher professional diploma a computer studies and a basic beginners Japanese language studies. Ina yin tallafi ta magana mai motsa rai, kuma ina bada kafaɗa ga iyaye masu yara dakeda buƙatu na musamman. Ni Ma'aikaciyar lafiyar kwakwalwa ce,kuma  mai ba da shawara ga yara masu bukata na musamman,kuma nice na kafa wani talk show “change the narrative”.  A cikin duk wannan tafiyar, na samu na zauna na tattauna da Tozali TV and magazine, Liberty TV, NTA Abuja and Arewa24 Kano da kuma BBC Africa.      
Patrick Jones - Course author