Canja Tsarin Kwalliya: Daga na Kullum zuwa na Shagali (How to go from Everyday Makeup to Glam Makeup)

  • Malama: Khadija Abdullahi Aminchi
  • Mataki: Mai sauƙi 
  • Sashe: 8 
Write your awesome label here.
Game da Darasi
Babu mace Mummuna sai macen da bata kwalliya. Kwalliya na nufin duk wani abunda za a ɗora a jiki ko a fuska don kyan gani. Wannan darasi, ya kawo kwalliyar fuska daki-daki, daga gyara fatar fuska kafin farawa, sa foundation, hoda, jan baki har ma da kwalliyar da ake wa ido. Wannan darasi ya baje muku kayan kwalliyan da za a iya amfani da su a fai-fai don samun cikakken abunda ake buƙata.
  • Lokacin Bidiyo: 1:45:20mins 
  • Takardar Kammalawa: Akwai

Abubuwan da ke Ciki

  •  Bidiyon Kallo guda 8
  • Jarrabawa
  • Takardar Kammalawa

Game Da Wannan Darasin  

Wannan darasin na ƙunshe da kayayyakin kwalliya, yanda ake amfani da su don samun biyan bukata. ya bada kwalliya kala biyu, na dare da kuma na rana, wanda zai kawo sauƙi a rayuwar mai kwalliya.

Fahimta

A wannan darasin za a koyi Kwalliya kala biyu, wanda za a yi da rana da kuma wanda za a yi da dare. Za a san kayan da yakamata a yi amfani da su don kwalliya ta zauna raɗau ta yi kyau a fuska.

Darussan da ke Ciki

Ga Malamar Ku

Khadija Abdullahi Aminchi

Sunana Khadija Abdullahi Aminchi, an haife ni a Funtua na Jihar Kastina. Na yi karatun primary a Funtua, secondary school kuma a Ulul al-bab science secondary a Katsina, bayan nan nayi karatuna na jami’a a Arah academy a kasar egypt. Ni matar aure ce kuma ina da yara guda 2 duka kuma ni ma aikaciyar gwamnati ce. Tun ina karama nike son kwalliya. A 2012 na fara kallon youtube videos ina koyan yadda ake kwalliyar ina sayan kayan kwalliya kadan-kadan, na yi ta yi har hannu na ya fara Kwarewa. 2016 na fara kwalliya a matsayin sana’a, yanzu Alhamdulillah mutane da yawa sun sanni.
Patrick Jones - Course author