Ɗawisu sha kallo: Inganta Kyawun Fata (How to Make Body butter, Balms and oil infusions using natural products)
-
Malama: Samira G Abari
-
Mataki: Mai sauƙi
-
Sashe: Goma sha daya
Write your awesome label here.
game da darasi
Gyaran jiki na da matuƙar muhimmanci a rayuwa! Fatar jiki aba ce mafi soyuwa a jikin dan Adam, shiyasa kyautata gyara ta ke da muhimmanci. Kyan fata na bawa mutum Ƙwarin gwiwa, banda wannan, kula da fata na sa mutum ya ji daɗin jikinsa. Wannan darasin zai koyar da ku yanda ake haɗa mayukan gyaran jiki wanda suke da abubuwa mara canja fata sai ma gyara da sa fata ta yi haske.
-
Lokacin Bidiyo: 1:19:12hrs
-
Takardar Kammalawa: Akwai
Abubuwan Da Ke Ciki
-
Bidiyoyin Kallo Guda 11
-
Jarrabawa
-
Takardar Kammalawa
Game da Wannan Darasi
Gyaran jiki na da matukar muhimmanci a rayuwa! Fatar jiki ita ce ke fara bayyana da an hango mutum. Kyan fata na bawa mutum Ƙwarin gwiwa. Wannan darasin zai koyar da ku yadda ake haɗa mayukan gyaran jiki da na gashi wanda suke da natural products masu inganci da kuma lafiya a fatar mutum.
Fahimta
A wannan darasin zaku fahimci abun da yasa gyaran fata da kuma kyan fata yake da matukar amfani. Za ku fahimci amfanin mai a jikin mutun da kuma yadda ake anfani dasu.
Darussan Da Ke Ciki
Samira Garba Abari na da ra'ayin taimakon matasa dan su cimma burin su na samun fasaha. Tun 2015 samira take aiki a matsayin mai sana'ar kanta, taimakawa mata da 'yan mata wajen koya musu kwarewar aiki. Ta shiga kungiyar CORE development initiative inda take tallafawa 'yan mata wajen gano kwarewar su. Samira tana koya ma kwararru kwarewar ta wanda suke aikin cigaban al'umma da kasa. Ta kuma mai da hankali wajen wahayi da cigaban matasa wanda sukeda sha'awar hidimar jama'a wajan cimma burin su.
Patrick Jones - Course author