Ilimin Balaga Ga Matasa (Sex Education for Teenagers)

  • Malama: Lorewa Original
  • Mataki: Mai sauƙi 
  • Sashe: 7
Write your awesome label here.
game da darasi
Tatsuniya da sirrika sune ke dabaibaye da ilimin balaga. Wasu matasa suna tsoron sa yayin da wasu ba za su iya jira ba, amma duk wani matashi sai ya riske shi. Wannan darasin an tsara shi ne don taimakawa yara su haɓaka ilimi, ƙwarewa da himma a duk rayuwarsu don yin zaɓin lafiya game da balaga da kuma kula da jikinsu. Wannan darasin yazo da batutuwa akan ilimin balaga, jima'i, da haihuwa ta hanyar da ta dace matasa zasu iya fahimta.
  • Lokacin Bidiyo: 23:13 mins
  • Takardar Kammalawa: Akwai

Abubuwan Da Ke Ciki 

  • Bidiyoyin Kallo Guda 6 
  • Jarrabawa 
  • Takardar Kammalawa 

Game da Wannan Darasi

A dalilin karancin ilimin balaga yawancin yara basu san yadda zasu kare kansu ba. Wannan darasin yana dauke da bayanai akan yanda yara zasu saita iyakokin su, tsafta da lafiya, matsin lamba daga tsara, balaga, lalata da sauransu.

Fahimta

Musamman idan magana ya danganci jima'i da lafiyar jima'i, yara basa iya tattaunawa tare da iyayensu wanda hakan ba daidai bane. A ƙarshen wannan darasin, yara za su koyi yanda za su tattauna komai akan ilimin balaga da jima`i tare da iyayen su cikin kwanciyar hankali.

                                                          Darussan Da Ke Ciki

Lorewa Original

Darasin Lorewa, haɗaka don kawo ingantaccen bayani game da harshen Hausa da kalmomin Hausa. Tabbatar da isar da ilimi wanda babu tsakuwa cikinta.
Patrick Jones - Course author