Kiwon Dabbobi (Livestock Farming)
-
Malama: Khadija Abdullahi Zakaria
-
Mataki: Na Tsakiya
-
Sashe: 7
Write your awesome label here.
game da darasi
Kiwon dabbobi na ɗaya daga cikin ababen da aka gada tun Kaka da Kakanni. Sana'a ce mai tarin albarka wanda ba kowa ya sani ba sai wanda ya sa kan shi a ciki. Kiwon dabbobi na samar da nama, fata da madara don anfanin ɗan Adam, yana kuma samar da ƙashi, bayan-gida, hatta jini don sarrafa abubuwa masu yawa.
-
Lokacin Bidiyo: 30:38mins
-
Takardar Kammalawa: Akwai
Abubuwan da ke Ciki
-
Bidiyon Kallo guda 16
-
Jarrabawa
-
Takardar Kammalawa
Game Da Wannan Darasin
Wannan darasin na ƙunshe da cikakken bayani a kan kiwon dabbobi daban-daban. Shanu, tumaki da raguna na daga cikin dabbobin da ake kiwonsu wanda yake tattare da tarin albarka. A wannan darasin za a sanar da duk sirrukan da suke lulluɓe cikin kiwon waɗan nan dabbobi uku.
Fahimta
Wannan darasi na feɗe duk wani abunda ɗan Adam ke buƙatan sani kafin fara kiwon dabbobi. Abun da za a samu daga dabbobin, cutukansu da ma inda za a samu dabbobin don fara kiwonsu
Darussan da ke Ciki
Ga malamarku
Khadija Abdullahi Zakaria
Sunana Khadija Abdullahi Zakariya, haifaffiyar Faskari LGA, Katsina. Na karanci Human Physiology a degreena na farko, a jami'ar Ahmadu Bello University, Zaria. Ina da aure da yara Uku. Na fara harkar kiwon Dabbobi shekaru sha uku da suka wuce da taimakon babata da kuma karfin zuciyana, ina cikin membobin kiwon dabbobi na katsina.
Patrick Jones - Course author