Koyon Haɗa Jaka (Basics of Bag Making)

  • Malama: Khadija Hamma Umar
  • Mataki: Na Tsakiya
  • Sahe: Sashe 4
Write your awesome label here.
game da darasi
Ka gaji da sayen jaka? ka gaji da fidda kuɗi ka sayi jakunkuna ka rabar lokacin biki ko suna? A wannan darasin za ku koyi yanda ake haɗa jaka da purse kala-kala cikin sauƙi da kuma kaya kaɗan. Jaka na daga cikin abubuwan da mata ke ado da shi hakazalika yana ƙara wa ado armashi, hasali ma za a iya cewa mace in bata cika adonta da jaka ko purse ba bata yi fita na girma ba. Ku bi wannan darasi don samun sauƙin kuɗaɗenku.
  • Lokacin Bidiyo: 32:31mins
  • Takardar Kammalawa: Akwai

Abubuwan da ke ciki

  • Bidiyo na kallo guda 6
  • Jarrabawa
  • Takardar Kammalawa

Game Da Wannan Darasin 

Ana amfani da jaka wajen sa abubuwa masu mahinmanci dan gudun kar su faɗi ko kuma su ɓata, A wanan darasin za ku koyi yanda ake haɗa jaka har kala biyu.

Fahimta

A wannan darasin za ku koyi yanda ake haɗa purse har kala uku, da kayan aiki a sauwaƙe da kuma yan kaɗan.

Darussan da ke Ciki

Ga Malamar Ku

Khadija Hamma Umar

Khadija Hamma Umar ɗalibar makaranta ce a jami'ar Usman Dan Fodio, tana karantan Pharmacy. Ta koya haɗa jaka ne a wani hutu da ta zo har ya zama sana'arta yanzu.
Ta zo muku da wannan darasin ne domin kuma ku koya yanda ake haɗa jaka ta yanda zaka iya yi da kanka ba tare da ka biya kuɗi masu yawa wajen siya ba. 


Patrick Jones - Course author