Koyon Sana`ar Hannu na Gargajiya (Traditional Hand Craft)

  • Malama: Umaymah Aliyu Umar
  • Mataki: Na Tsakiya
  • Sashe: 5
Write your awesome label here.
game da darasi
Kuna ganin abubuwan gargajiya masu kyau da ƙyalli amma ba ku san yanda za ku yi da kanku ba? Ku na so ku yi lallen gam (cellotape) a gidajenku amma ba ku iya ba sai dai ku fita ku je gidan lalle? To ga dama ta samu da za ku yi abunku a gida da kanku ba tare da kun fita waje ba.
  • Lokacin Bidiyo: 03:12:36hrs 
  • Takardar Kammalawa: Akwai

Abubuwan Da Ke Ciki

  • Bidiyo na kallo guda 12
  • Jarrabawa
  • Takardar Kammalawa

Game Da Wannan Darasin

A zamanin da sun ɗauki sana`ar hannu abu mai muhimmanci, Saɓanin yanzu da abubuwan zamani na turawa suka shige mu. Wannan darasin namu yana ɗauke da abubuwan gargajiya da idan ka koye su za su maka amfani sosai.

Fahimta

A wannan darasin za ku koyi yanda ake mafici, yanda ake kayan ƙyale-ƙyale yanda ake kwaɓa lalle, har ma da yanda ake yanka cellotape na lallen.

Darussan da ke Ciki

Ga Malamarku

Umaymah Aliyu Umar

Umaymah Aliyu 'yar kasuwa ce, tana sana`o`i masu yawa na gargajiya. Ta ƙware a wajen yin abubuwan gargajiya da kanta domin kasuwancin ta. Ta zo muku da wannan darasin domin ku koyi abubuwan gargajiya domin yin sana`ar shi ko kuma don amfaninku na yau da kullum 

Patrick Jones - Course author