Kula da Lafiya Lokacin Al`ada (Menstrual Health and Well-being)

  • Malama: Zainab Ibrahim Hashim
  • Mataki: Na Tsakiya
  • Sashe: 6 
Write your awesome label here.
Game da darasi
Kula da lafiya lokacin al`ada ga ya` mace  wajibi ne a gare mu saboda gujewar kamuwa da cuta. A wannan darasin zaku ji  bayanai masu muhimmanci da suka shafi yanda zaku kula da yanki mai zaman kansa da kuma tsaftar jikin ku, cututtukan da za ku iya kamuwa da su yayin al`ada  har  yanda za ku dinga gane lokacin da yakamata al`adan ya zo.
  • Lokacin Bidiyo: 28min 
  • Takardar Kammalawa: Akwai

Abubuwan da ke Ciki

  • Bidiyoyi na Kallo Guda 12
  • Takaddar Karin Bayani 
  • Jarrabawa 
  • Takaddar Kammalawa

Game Da Wannan Darasi 

Mata dayawa suna al`ada ne kawai ba tare da sun san abubuwan da za su yi dan kula da jikinsu ba,  da yawan mata za ku ga basu san awa nawa audugan mata yakamata ya dinga yi jikinsu ba kafin su cire, wasu ma sai su wuni da guda daya tun safe har dare wanda idan ba a yi wasa ba zai iya haifar da wani ciwo babba a jikin mutum.

Fahimta

Yakamata kowacce mace ta san kula da jikinta lokacin al`ada yana da matukar amfani a cikin rayuwarta, tasan abubuwan da ya kamata ta yi da wadanda ya kamata ta bari a lokacin al`adanta.

Darussan Da Ke Ciki 

Ga Malamar Ku 

Zainab Ibrahim Hashim 

Zainab Ibrahim Hashim matashiya ce mai fadakarwa akan duk abunda ya shafi lafiyar jiki musamman ma yan`mata masu tasowa. Tazo muku da wannan darasin ne domin ku fahimci yanda zaku kula da kanku lokacin al`ada domin rashin kula da jiki yayin al`ada kan iya haifar da cututtuka kala kala a jikin dan adam.

Patrick Jones - Course author