Kyautan Karshen Shekaran Ku Ya Iso. Darussa 30 a farashin N2,500.00
Matakan Zama Kwararre a Zanen Dinki (Blueprint for Becoming a Fashion Illustrator)
-
Malama: Ruqayya Ibrahim Ahmad
-
Mataki: Mai sauƙi
-
Sashe: 11
Write your awesome label here.
game da darasi
Ɗinkin atamfa ga macen Arewa shine abu na farko da ake dubawa lokacin fita, don yana ɗaya daga cikin abubuwan da ke ƙara izza da nuna mace ta kai. Wannan Darasi ya koyar da zanen ɗinki daga tushensa, manhaja da za a iya zane da su, ire-iren zane da ma yanda ake sa atamfa a kan zane. Darasi ne wanda yake da duk wani abunda mai son fara zane zai yi anfani da su don zama ƙwararre cikin lokaci ƙanƙani.
-
Lokacin Bidiyo: 2:12:00hrs
-
Takardar Kammalawa: Akwai
Lorewa Year End Promo
Lorewa is opening up 30 Courses for just N2,500.00.
Abubuwan Da Ke Ciki
-
Bidiyoyin Kallo Guda 18
-
Jarrabawa
-
Takardar Kammalawa
Game da Wannan Darasin
Wannan darasin zai sadaku da duniyar zane, zai fayyace zare da abawar da a kullum muke hasashen sanin ta ya ya. Zai koyar da yanda ake fara zane, yanda ake wahalar yi a takadda da kuma sauƙin da muka samu na na'urorin zamani.
Fahimta
A cikin darasin nan za ku san applications daban-daban, za ku san Ibis paint da aikinsa a duniyar zane. Sa atampa a kan zanen jiki da ma ɗora ɗan kwali da ɗan kunne.
Darussan da ke Ciki
Ruqayya Ibrahim Ahmad
Na kasance mai son zane da kuma sutura masu ƙayatarwa, kuma tun lokacin da na gane zan iya haɗasu wuri guda na tafi University of Arts
da ke London da kuma London College of Fashion na ɗauki darussansu na yanar gizo. Tun 2019 na fara aiki da manyan masu ɗinki a Najeriya, kama daga Atamfa, material ko kayan amare. Daga baya na zauna don yi wa kaina aiki. Ina son abunda nake yi, don idan bana zane, to fa karatu nake yi don a yanzu ina karantar likitanci da hanyoyin kula da asibiti. Na kawo wannan darasin ne don ina jin daɗin mayar da ɗigo zuwa wata tsari na daban wanda mutum zai iya sawa ya yi kyau.
Patrick Jones - Course author