Sana'ar Gwanjo (Business Of Thrifting)

  • Malama: Rashida Idris
  • Mataki: Na Tsakiya
  • Sashe: 7
Write your awesome label here.
Game da darasi
Abaya kaya ne da mafi yawan matan arewa ke jin daɗin anfani da su, kaya ne wanda ba shi da takura bare nuna jiki. Wannan darasi zai yi bayani akan abubuwan da mutum ya kamata ya sani kafin ya fara sana'ar gwanjo na abaya. Za a koyi yanda ake samowa, sa kuɗi, mu'amala da masu saye, rarrabe kaloli da waɗanda za su iya yin sana'ar abaya.

  • Lokacin Bidiyo: 20:42mins
  • Takardar Kammalawa: Eh

Abubuwan Da Ke Ciki 

  • Bidiyoyin Kallo Guda 6 
  • Jarrabawa 
  • Takardar Kammalawa 

Game da Wannan Darasi

Wannan darasin na koyar da yanda za a fara sana'ar gwanjo, abubuwan da ake buƙata kafin farawa, abunda za a tarar, yanda za a rarrabe, yanda za a sa musu kuɗi da yanda za a yi mu'amala da masu saye.

Fahimta

A wannan darasin za a samu cikakken bayani game da gwanjo, inda ake samar wa da dabarun da zai kawo ci gaba a sana'ar.

                                                          Darussan Da Ke Ciki

Ga malamarku

Rashida Idris Maikampa

Rashida Idris 'yar jihar Plateau ce, Wase L.G.A. Ta ƙware a sana'ar gwanjon abaya, hakan ya sa ta koyar da dabarun sana'ar. Ta yi makaranta a Nasarawa State University, inda ta karanci Biology, haka kuma ta yi degree nata na biyu a fannin psychology.
Patrick Jones - Course author