Waraka Ga Zawarawa (Path To Healing After Divorce)

  • Malama: Khadija Ibrahim
  • Mataki: Na Tsakiya
  • Sashe: 7
Write your awesome label here.
Game da darasi
Mutuwar aure ba ƙarshen rayuwa ba ce. A Arewacin Najeriya da yawa aure na mutuwa, kuma da yawa ba su san yanda za su ci gaba da rayuwa ba bayan aure ya mutu. Ke mace ce da aurenki ya mutu kuma ba ki san yanda za ki ci gaba da rayuwa ba? Ko kina da 'yar uwa da aurenta ya mutu amma kullum tana cikin damuwa? Ku biyo mu a wannan darasin domin sanin yanda za ku samu waraka daga damuwar da mutuwar aure ke haifarwa.
  • Lokacin Bidiyo: 54:16
  • Takardar Kammalawa: Akwai

Abubuwan Da Ke Ciki

  • Bidiyoyi na kallo guda 9
  • Jarrabawa
  • Takardar Kammalawa

Game Da Wannan Darasin

Mata da yawa idan aurensu ya mutu suna shiga matsanancin damuwan da zai hana su walwala da sukuni, wanda hakan sosai ke kawo nakasa ga ci gaban rayuwarsu. A wannan darasin za ku ji abubuwan da yakamata ku bi domin gujewa shiga  damuwa.

Fahimta

A wannan darasin za ku fahimci shiga damuwa bayan mutuwar aure ba abun so bane. Wannan darasin ya zo muku da abubuwan da idan kun bi za ku samu waraka daga zawarci.

GA MALAMARKU

Khadija Ibrahim

Khadija Ibrahim ƙwararriyar mai bada shawara ce. Ta ƙware wajen aikinta hakan ya sa ta zo muku da hanyoyin da zawarawan da suke cikin damuwa za su samu waraka  har su yi rayuwa cikin annashuwa.
Patrick Jones - Course author