Yanda Ake Bude Kungiyar Tallafawa Al'ummah na Zaman Kansa (NGO)- (How to start an NGO)

  • Malama: Fatima Habib
  • Mataki: Na Ƙoli 
  • Sashen:3
Write your awesome label here.
game da darasi
Kuna son ku fara tallafawa al`umma marasa karfi? Kuna so ku bude kungiyar ku mai zaman kansa domin tallafawa al`umma da dama? Wannan darasin namu yana dauke da duk wani bayani da zaku bukata domin ganin kun cimma wannan burin naku na taimakawa al`umma a fadin kasan nan.
  • Lokacin Bidiyo:17min 
  • Takardar Kammalawa: Akwai

Abubuwan da ke ciki

  • Bidiyo na Kallo Guda 3
  • Jarrabawa
  • Takardar Kammalawa

Game Da Wannan Darasi

Kungiyar tallafawa al`umma kungiya ce mai zaman kansa wanda suka kware wajen tallafawa al`umman duniya baki daya, mutane dayawa suna son su bude kungiyar tallafawa al`umma domin suyi taimako a garuruwa dayawa amma basu san yanda zasu bi su bude ba.

Fahimta

A wannan darasin zaku ji yanda ake yi a bude kungiyar tun daga farkon ta har zuwa abubuwan da zakuyi domin kafa taku kungiyar da kuma hanyoyin da zakubi domin samun cigaba a harkar taimako da kuma kare kungiyar taku daga wani wanda yayi niyyan amfani da abubuwan da kukeyi domin yin damfara wa mutane.

Darussan da ke Ciki

Fatima Habib

Fatima yar borno ce wanda itace CEO (UWAR) kungiya me zaman kanta  Advocacy for human life foundation. Ta fara wannan kungiyar ne tun tana yar shekara goma sha hudu. Fatima ta gudanar da manyan project guda goma sha biyar a fadin Najeriya wanda ya tabi rayukan duban mutane. Ita ce mace ta farko wanda ta fara aiki akan yaki da jahilci a arewacin Najeriya, kuma mace ta farko wanda ta shugabanci zangazanga akan dawo da yaran Chibok a borno.
Patrick Jones - Course author