Zanen Dinki (Fashion Illustration for Beginners)
-
Malama: Ramatu Walida Shehu
-
Mataki: Na Tsakiya
-
Sashe: 5
Write your awesome label here.
game da darasi
Mutane da dama suna dauka zanen ɗinki da ɗinki duk abu daya ne, amma abun ba haka yake ba. Zanen ɗinki tsarin shi daban da na tela. Tela shine mai ɗinkawa. Mai zanen ɗinki kuma shine mai zanen ɗinki kamarsu riga da skirt ko dogon riga da sauran su kafin a kaiwa tela ya ɗinka. A wannan darasin zaku koyi yanda ake amfani da nau'rorin zamani ayi zanen ɗinki kala kala ya fito yayi ras dan kaiwa tela yayi maka samfur din.
-
Lokacin Bidiyo: 46mins
-
Takardar Kammalawa: Akwai
Abubuwan Da Ke Ciki
-
Bidiyoyi Na Kallo 5
-
Jarrabawa
-
Takardar Kammalawa
Game Da Wannan Darasi
Wannan darasin na dauke da bayanai akan yanda ake zana ɗinki kamarsu, riga da skirt harma dogon riga da dankwali. Kuma darasin zai koya muku yanda zaku kware wajen zanen ɗinki akan na'uran zamani na ipad.
Fahimta
A wannan darasin zaku koyi yanda ake zanen ɗinki dan yiwa kai da kuma yi don sana'a da sauran su.
Darussan da ke Ciki
Ramatu Walida Shehu
Ramatu Walida Shehu mai zanen ɗinki ce. Kuma ta kware wajen zanen ɗinki akan na`uran zamani na ipad. Tana da shafin yanar gizo na Instagram inda zaku iya bi kuma kuna ganin design din kayayyakin ta. Ta kawo muku wannan darasin domin kuma ku koyi zanen dinki ba sai kun dinga shan wahala wajen neman samfur din ɗinki a wajen mutane daban daban ba.